Brazil 2014: Karin kasashe sun tsallake

Asamoa Gyan
Image caption Asamoa Gyan ya fara ci wa Ghana

Karin kasashe bakwai sun samu gurbi a gasar Kofin Duniya da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Daga Turai mai rike da Kofin Spain da Ingila da Rasha sun tsallake yayin da a karon farko Bosnia ta samu dama.

Chile da Ecuador su ne na baya bayan nan da suka samu gurbin daga Latin Amurka.

Yayin da Honduras ta samu gurbi na kai tsaye na karshe na yankin Amurka ta tsakiya da ta arewa.

Mexico kuwa ta samu damar zuwa matakin wasan fitar da gwani na zuwa gasar ta Kofin Duniya ne bayan da Amurka ta ci Panama kwallaye biyu.

A Afrika kuwa Ghana ta kama hanyar zuwa Brazil din bayan da ta lallasa Masar da ci 6-1 a karawar farko tsakaninsu a Kumasi.

Bayan haduwa ta biyu a ranar 19 ga watan Nuwamba ne za a san wadda za ta je gasar.