Hodgson: "Ina alfahari da Ingila"

Image caption Roy Hodgson

Roy Hodgson ya ce tsallakewa zuwa gasar cin kofin kwallon duniya a Brazil shine abin alfaharinsa a tarihin kwallon kafarsa.

Ingila ta samu gurbin zuwa gasar, bayan ta doke Poland a filin Wembley daci 2-0.

Wayne Rooney da kyaftin Steven Gerrard ne suka tabbatarwa Ingila gurbinta a gasar.

Hodgson mai shekaru 66, ya jagoranci Switzerland a gasar cin kofin duniya a Amurka a shekarar 1994, amma kasar bata taka rawar gani ba.

Hodgson yace " Ni dan Ingila ne kuma ina alfahari da hakan".

Ingila ta kasance ta farko rukunin H inda ta samu maki 22 cikin wasanni 10.

Karin bayani