Masar ba za ta kori kocinta Bradley ba

Bob Bradley
Image caption Kocin Masar dan Amurka

Masar ba za ta sallami kocinta Bob bradley ba, bayan casa su da Ghana ta yi daci 6 -1, a wasan neman shiga gasar kofin duniya da suka kara a Kumasi.

Shugaban hukumar kwallon Masar Gamal Allam ya ce "idan muka sallame shi za mu biya shi kimanin fan 230,000 kuma bamu shirya haka ba".

Bradley ba zai jagoranci karawa ta biyu a Alkahira ba, sakamakon fargabar tsaron lafiyarsa.

Allam na da tabbacin magoya baya baza su bari Bradley ya jagoranci wasa na biyu ba, saboda haka an shirya mataimakin sa Diaa El Sayed zai jagoranci karawar ta biyu, a ranar 19 ga watan Nuwamba.

Yayin da duk wani fata da Masar ke da shi na samun gurbin zuwa gasar kofin duniya a Brazil kusan ya kare.