Bale ya koma horo a Real Madrid

Image caption Gareth Bale

Dan kwallon da yafi kowanne tsada a duniya, Gareth Bale ya koma horo tare da Real Madrid, kuma watakila ya buga wasa tsakaninsu da Malaga a ranar Asabar.

Dan wasan da aka saya daga Tottenham a kan fan miliyan 85.3 bai bugawa Wales wasa tsakaninta da Belgium ba, saboda a cinyarsa, kuma tun da ya koma Real, sau uku kawai ya bugawa kulob din wasa.

Dan shekaru 24, ya yi horo tare da tawagar a Spain a ranar Lahadi.

A kwanakin baya ne, Real Madrid ta karyata zargin cewar Bale na fama babban rauni a kafarsa.

Karin bayani