Razak ya koma Anzhi Makhachkala

Image caption Abdul Razak ya bugawa Ivory Coast kwallo sau 7

Dan kwallon Manchester City, Abdul Razak ya koma Anzhi Makhachkala ta Rasha.

Dan Ivory Coast din, ya tafi a matsayin aro ne a Rasha, kafin ya kulla yarjejeniyar dun-dun-dun da kulob din.

Razak ya hade da Manchester City ne daga Crystal Palace a shekara ta 2010.

Cikin shekaru uku da ya shafe a City wasanni bakwai kadai dan kwallon mai shekaru 20 ya buga.

A baya ya taba tafiya aro a Portsmouth, Brighton da kuma Charlton.