Messi da Puyol za su komawa Barca

Image caption Gwarzon dan kwallon duniya, Lionel Messi

Dan kwallon Barcelona Lionel Messi, zai koma taka leda a ranar Asabar a wasansu da Osasuna.

Messi mai shekaru 26, ya samu rauni a watan Satumba a wasan Barca da Almeria.

Shima Carles Puyol shima ya murmure bayan shafe watanni shida yana jinyar rauni a idon sawunsa.

Sai dai Dani Alves, Alexis Sanchez da kuma Gerard Pique duk suna jinyar rauni, a don haka ba zasu buga wasan Barcelona da AC Milan da kuma karawarsu da Real Madrid a gasar La Liga.

Karin bayani