Kwallon Wilshere ya burge ni — Wenger

Jack Wilshere
Image caption Kwallon da ya zura tana daga cikin wacce tayi fice

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kwallon da Jack Wilshere ya fara zura wa Norwich a wasan da suka lashe da ci 4-1 na daya daga cikin kwallayen da aka zura da suka kayatar da shi.

Wenger ya ce "Dukkan kwallayen da aka zura sun kayatar, amma kwallon farko na daban ne kuma ya ba mu kwarin-gwiwa"

Hakika kwallon ya burge ni, saboda sai da aka shirya wasa har aka zura a raga.

Wilshere mai buga tsakiya mai shekaru 21, shi ya zari kwallo daga tsakiya ya bai wa Carzola daga hagu, daga baya suka yi ba-ni-in-ba-ka shi da Giroud kafin ya zura kwallo a raga cikin ruwan sanyi.

Wannan shi ne karo na farko da ya zura kwallo a gasar Premier a filin Emirate, kuma kwallon ya taimaka wa Arsenal darewa kan teburin Premier da tazarar maki biyu.