Adamu zai dawo gudanar da Kwallo

Amos Adamu
Image caption Yanzu yana da damar dawowa harkar wasan kwallo

Tsohon dan kwamimitin Amintattu na hukumar Fifa Amos Adamu ya cika tatunkumin da aka sa masa a kan kwallon kafa na shekaru uku.

Dan Nigeriya an dakatar da shi ne saboda ya nemi a bashi kudi kafin ya kada kuri ar zaben kasar da za ta karbi bakuncin gasar duniya ta 2018 da 2022.

An dauke shi a fefen bidiyo yana tambayar kimanin dala 800,000, aka kuma hana shi kada kuri ar zaben 2010.

Adamu, zai iya dawo wa harkar kwallon kafa tun da ya kammala takunkumin da ya zo karshe ranar Lahadi data gabata ya ce" godiya nake da kammala takunkumin kuma bani da haufi akan kowa.