Ingila za ta fafata da Denmark

Image caption 'Yan wasan Ingila suna samun horo

Ingila za ta kara da Denmark a wasan sada zumunta a filin wasa na Wembly, a shirye-shiryen da take yi na tunkarar Gasar cin kofin duniya a shekarar 2014.

An shirya wasan ne cikin yarjejeniyar da kasashen suka cimma, suka kara a Copenhagen a watan Febrairu shekarar 2011.

Ingila za kuma ta kara da Chile da Jamus a Wembley a wasannin sada zumunta domin tunkarar kofin duniya a Brazil shekara mai zuwa.

Rabon da kasashen su kara a gasa, tun gasar kofin duniya na 2002.

Ingila ta lashe wasan da kwallaye uku da nema.