Brazil: Faransa za ta kara da Ukraine

European Qualifier
Image caption Tikiti hudu ya rage a Nahiyar Turai zuwa Brazil

Tsohuwar Gwarziyar kofin duniya, wato Faransa za ta kara da Ukraine a wasan cike gurbin nahiyar Turai na shiga kofin duniya a shekarar 2014.

Portugal za ta kara da Sweeden, hakan na nufin tsakanin Christiano Ronaldo da Zlatan Ibrahimovic daya ba zai sami halartar gasar kofin duniya a Brazil ba.

Iceland da ke kasan tebur a kasashen da suka fi iya kwallo a duniya sai ta doke Croatia sannan ta samu damar shiga gasar cin kofin duniya a karon farko, inda Greece za ta kara da Romania.

Wasannin da za a kara gida da waje, za a fara karawa ranar 15 da 19 ga watan Nuwamba.

Portugal v Sweden

France v Ukraine

Greece v Romania

Iceland v Croatia