Dortmund ta doke Arsenal da ci 2-1

Arsenal vs Dortmund
Image caption Dortmund ta sami kwarin gwiwa da ta lashe Arsenal

Kungiyar Borussia Dortmund ta sami nasara a kan Arsenal har gida daci 2-1 a gasar kofin zakaru ta Nahiyar Turai.

Dan wasan Dortmund Henrikh Mkhitaryan shi ya fara zura kwallo a minti na 16, Arsenal ta farke kwallo a minti na 46 ta hannun Olivier Giroud.

Ya rage saura minti takwas a tashi wasa Robert Lewandowski ya zura wa Arsenal kwallo a raga.

Sauran sakamakon wasannin

Celtic v Ajax Schalke 0 v Chelsea 3 Marseille 1 v Napoli 2 Milan 1 v Barcelona 1 Steaua Bucharest 1 v Basel 1 FC Porto 0 v Zenit St Petersburg 1 FK Austria Vienna 0 v Atl├ętico Madrid 3