A kyale Bale ya sarara - Ronaldo

Ronaldo and Bale
Image caption Ronaldo yana taya Bale murnar zura kwallo

Cristiano Ronaldo ya damu da yadda ake matsawa dan kwallon da Madrid ta saya mafi tsada Gareth Bale.

Bale mai shekaru 24 dan Wales, ya zira kwallo daya tal tun lokacin da ya koma Madrid.

Ronaldo ya ce "Bai kamata mu matsa masa ba, hakan ba zai kuma taimaka masa ba, yana iya kokarinsa kuma yana murnar zuwan sa Madrid".

Bale ya zura kwallo a wasan farko da ya bugawa Madrid a watan Satumba, bayan da aka sayo shi daga Tottenham amma rauni ya hana shi buga wasanni.