'Dalilin da yasa Beckham ya bar United'

Alex Ferguson
Image caption Tsohon managan United Sir Alex Ferguson

Tsohon kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce tsohon kyaftin din Ingila David Beckham ya bar kungiyar ne bisa dalilin dan wasan yana ganin gaba yake da kungiyar.

A sabon littafin da ya wallafa, Ferguson ya ce ya sami sabani da Beckham bayan da ya zargeshi da rashin kokari a wasan kofin kalubale, da Arsenal ta samu nasara a kan United a shekarar 2003

Ferguson ya kara da cewa na damu da yadda Beckham yake gudanar da rayuwar sa, musamman da ya auri Victoria Adam, ta kungiyar mawakan 'Spice Girls'.

David ne dan wasan dana horar wanda ya zabi komawa fitaccen dan wasa, ya kuma kudurta a sanshi ta bangaren da ba kwallon kafa ba.

Beckham ya lashe kofin Premier shida, kofin kalubale biyu da kofin zakarun Turai daya lokacin yana United kafin kungiyar ta sayar dashi Real Madrid kan kudi fan miliyon 25 a shekarar 2003.

'Takun saka da Rooney'

Ferguson ya kara da cewa ya dawo daga rakiyar Rooney dab da zai bar kungiyar saboda baya kokari. Sannan yaki karbar aikin horadda Ingila har karo biyu.

Ya kuma ce, Cristiano Ronaldo shine dan kwallon da ya horar dan baiwa, har ma ya fada masa gwara ya harbe shi maimakon ya sayar dashi ga Real Madrid.

A cewarsa, ya samu rashin jituwa da Rafael Banitez saboda ya nemi cin zarafinsa.

Kuma dakatar da Ferdinand watanni takwas sakamakon kin zuwa gwajin kwayoyi yayi tsauri a shekara ta 2003.

Ya kuma bayyana Roy Keane cewar matsalar sa bakinsa, yana da munanan kalamai a bakinsa da ba zaka taba yadda zai fada ba.

Ya kuma ce Ingila baza ta dauki kofin duniya ba, har sai ta samu 'yan wasa 'yan baiwa kamar na Brazil.

Sir Alex Ferguson ya shafe shekaru 26 yayi a United, inda ya lashe kofina 38, ya kuma horadda zakakuren 'yan wasa da suka hada da Beckham da Eric Cantona da Cristiano Ronaldo da Peter Schmeichel da Bryan Robson da Roy Keane da Jaap Stam da kuma Ruud Van Nistelrooy.