Ghana ta sake neman dage wasa

ghana Team
Image caption Kungiyar kwallon kafa ta Ghana Black Stars

Ghana ta sake bukatar Fifa a karo na biyu ta dauke wasan da za ta buga da Masar daga birnin Alkahira.

Fifa ta nemi Masar ta kyautata tsaro sannan ta ba ta tabbacin cewa komai zai kasance cikin tsari a lokacin wasan kafin 28 ga watan Oktoba.

Da ma dai Ghana ta nemi a dage wasan ne ranar 19 ga watan Nuwamba.

'Yan wasan Ghana, da suka sami nasara a wasan farko da ci 6-1, sun bayyana damuwarsu kan yanayin tsaron Masar.

Shugaban kwallon kafa ta Ghana, Kwesi Nyantaki, ya ce "ba za mu jefa rayuwar 'yan wasa da jami'ai da magoya bayanmu cikin hatsari ba''.