Holloway ya bar Crystal Palace

Ian Hollaway
Image caption Ian Hollaway tsohon kocin Crystal Palace

Kocin Crystal Palace, Ian Hollaway, ya bar kungiyar kasa da shekara guda bayan nada shi a kan mukamin.

Sai dai kungiyar ba ta fitar da wata sanarwa domin nuna cewa kocin, mai shekaru 50 a duniya, ya bar ta ne domin radin kansa ko sallamarsa ta yi ba.

Hollaway ne ya jagoranci Palace shiga gasar Premier, tun lokacin da ya koma kungiyar a watan Nuwamba 2012.

Ya samu nasara a wasa daya yayin da ya sha kaye a wasanni bakwai.

Rashin nasarar da kungiyar ta yi da ci 4-1 a hannun Fulham ya sanya ta koma kasan Tebur.