Madrid ta lashe Juventus da ci 2-1

Madrid vs Juventus
Image caption An zura kwallaye a gasar kofin zakarun Turai

Kungiyar Madrid ta samu nasara akan Juventus daci 2-1, a gasar kofin zakarun Turai.

Dan kwallon Madrid Criastiano Ronaldo shi ya fara zura kwallo a minti na 4 da fara wasa, sai a minti na 22 Fernando Llorente ya farkewa Juventus kwallo. Daga baya Ronaldo ya kara kwallo ta biyu a dukan daga kai sai mai tsaron raga.

Sauran sakamakon wasannin

CSK Moskva 1 vs Manchester City 2 Manchester United 1 vs Real Sociedad 0 Bayer 04 Leverkusen 4 vs FC Shakhtar Donetsk 0 Bayern Munich 5 vs FC Viktoria Plzen 0 Galatasaray 3 vs FC Kobenhavn 1 Anderlecht 0 vs Paris Saint-Germain 5 Benfica 1 vs Olympiacos 1