Afrika ta Kudu za ta kara da Spain

Image caption Magoya bayan Bafana Bafana a Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu za ta kara da zakarun kwallon duniya wato Spain a wasan sada zumunci a Johannesburg a ranar 19 ga watan Nuwamba.

Shugaban hukumar kwallon Afrika ta Kudu, Safa, Dr Danny Jordaan ya ce wasan zai kayatar saboda dama ce ga tawagar Bafana Bafana ta kara da manyan 'yan wasa irinsu Iniesta da Xavi.

Jordaan ya kara da cewar " za a buga wasan a filin Soccer City inda aka buga gasar kwallon duniya na farko a nahiyar Afrika".

Shugaban hukumar kwallon Spain, Angel Maria Villar Llona ya ce "mun zaku mu koma Afrika ta Kudu inda muka dauka kofin gasar kwallon kafa ta duniya a karon farko a tarihin kwallonmu".

Karin bayani