"Bale ya taka rawa da barcelona"

Gareth Bale
Image caption Wasa na biyu da ya bugawa Madrid a karawa da Barcelona

Kocin Real Madrid Carlo Arcelotti ya kare Gareth Bale, duk da rashin kokarinsa a karawar da su ka yi da Barcelona.

Bale, mai shekaru 24 ya buga wasan a zaman mai kai kora, gurbin da ba a san yana bugawa ba, a wasansa na biyu da Madrid bayan da jinyar rauni ya hana shi buga kwallo.

Bayan wasan da ya fafata na awa guda Karim Benzema, ya canja dan wasan da aka saya a kan kudi kimanin fam miliyon 85.

Bale, ya koma Madrid a zaman dan kwallon da ya fi tsada a duniya daga Tottenham, sai dai raunukan tafin kafa da cinya sun hana shi buga kwallo a kai - a kai.

Ancelotti ya ce "Wannan shi ne wasan da suka kara tare da 'yan wasa, kuma sai a hankali zai lakanci wasa tare da su, kuma hakan ya na faruwa ga kowanne dan wasa."