Chelsea ta doke Manchester City

Chlsea vs Manchester City
Image caption Chelsea tana matsayi na biyu a teburin Premier

Kungiyar Chelsea ta doke Manchester City da ci 2-1 a gasar Premier wasan mako na tara, kuma sakamakon ya bai wa kungiyar damar zama ta biyu a teburin Premier.

Dan kwallon Chelsea Andre Schurrle shi ya fara zura kwallo a ragar Manchester City, bayan an dawo daga hutu Manchester City ta farke kwallo ta hannun dan wasanta Sergio Aguero.

Daf da za a tashi mai tsaron bayan City Matija Nastasic, ya maida kwallo gida da ka, amma golan City Joe Hart ya fito daga raga suka yi karo kwallo ta zagaye Fernando Torres ya zura kwallo a raga.

Har yanzu Arsenal tana matsayi na daya da maki 22, Chelsea da Liverpool suna matsayi na biyu dana uku da maki 20 kowannensu. Manchester City na matsayi na bakwai da maki 16, makwabciyar ta mai rike da kofin Premier Manchester United tana matsayi na 8 da maki 14.