Fifa: A tsaurara matakai kan wariya

Sepp Blatter
Image caption Sai mun dauki tsauraran matakai kafin a kawar da wariya a kwallon kafa

Sepp Blatter ya nemi a dauki tsauraran matakai don kawar da wariya a wasan kwallon kafa, da za su hada da korar kungiyoyi da diban maki.

Kwamitin ladabtarwa na UEFA ya fara sauraren kara a kan CSKA Moscow da dan wasan Manchester City Yaya Toure ya yi zargin 'yan kallon kungiyar sun yi masa kalamun wariya.

Shugaban Fifa Blatter, ya ce matakan cin tarar kungiya ko tursasa wa kungiya wasa babu 'yan kallo ba su wadatar ba.

A lokacin da yake jawabi a taron hukumar na cikar shekaru 150 a Londan, Blatter, ya ce "ya kamata mu kori kungiya ko kwace maki a lokacin gasa, da wannan mataki za mu iya kauda kyama da nuna wariyar launin fata.