A fadada gasar cin kofin duniya- Platini

Image caption Michel Platini

Shugaban hukumar kwallon Turai, UEFA Michel Platini ya ce yanason a kara yawan kasashen dake fafatawa a gasar cin kofin duniya daga kasashe 32 zuwa 40.

Platini ya yi wannan kira ne bayan da Shugaban Fifa, Sepp Blatter ya ce ya kamata a karawa kasashen Afrika da Asiya gurbin zuwa gasar, sannan kuma a ragewa kasashen Turai.

Platini yace "a maimakon ragewa kasashen Turai gurbinsu, a maida gasar ta koma ta kasashe 40 mana".

An buga gasar cin kofin duniya na farko a shekarar 1930 tare da kasashe 13, sannan suka koma 16 a shekarar 1934 sai kuma suka koma 24 a shekarar 1982 a yayinda kasashe 32 suka fafata a shekarar 1998.

Karin bayani