AS Roma ta kafa tarihi a gasar Serie A

Image caption 'Yan tawagar Roma a Italiya

Kungiyar AS Roma ta Italiya ta kafa sabon tarihi a gasar Serie A bayan data samu galaba a wasanni tara cikin karawa tara data yi.

A cikin wasannin tara, sau daya tal aka zira kwallo a ragar Roma, inda take da maki 27.

Roma ta baiwa Napoli da Juventus tazarar maki biyar a saman jadawalin gasar kwallon Italiya kawo yanzu.

A baya Juventus ce ta kafa tarihi inda ta samu nasara a wasanni takwas cikin takwas amma a yanzu Roma ta shiga gaba.

Wasannin da Roma ta buga:

25 Aug: Livorno 2-0

01 Sep: Verona 3-0

16 Sep: Parma 3-1

22 Sep: Lazio 2-0

25 Sep: Sampdoria 2-0

29 Sep: Bologna 5-0

05 Oct: Inter Milan 3-0

18 Oct: Napoli 2-0

27 Oct : Udinese 1-0