Arsenal Ta Dauki Serge Gnabry

Serge Gnabry
Image caption Dan kwallon da Arsenal ta ke sa ran zai zama gwarzo

Dan kwallon Arsenal mai wasa a gaba Serge Gnabry ya amince da sabuwar yarjejeniya da kungiyar da take matsayi na daya a teburin Premier.

Dan wasan mai shekaru 18, ya fara wasa lokacin da Arsenal ta kara da Stoke City a watan Satumba, ya kuma zura kwallonsa na farko a wasan Swansea a cikin watan jiya.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya sanar a shafin internet na kungiyar cewa "Mun dauki Serge Gnabry, saboda muna da yakinin zai zama fitaccen dan wasa."

Gnabry ya canji Mathieu Flamini a wasan da suka kara da Crystal Palace a ranar Asabar da ta gabata, fawul din da aka yi masa Arsenal ta samu Penarity a wasan da suka lashe da ci 2-0.