Chelsea ta doke Arsenal da ci 2-0

Arsenal vs Chelsea
Image caption Chelsea ta kai wasan kungiyoyi takwas na gasar

Kungiyar Chelsea ta doke Arsenal har gida da ci 2-0 a gasar kofin Capital One na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Dan kwallon Chelsea Cesar Azpilicueta shi ya fara zura kwallo a minti na 25, sai Juan Mata ya kara kwallo ta biyu a minti na 66.

Da wannan sakamakon an shire Arsenal daga gasar Bana, yayinda Chelsea ta kai matakin kungiyoyi takwas da zasu fafata a wasan gaba.

Sauran sakamakon wasanni

Burnley 0 vs 2 West Ham United Manchester United 4 vs 0 Norwich City Leicester City 4 vs 3 Fulham