Zamu iya lashe gasar Premier - Ferguson

Alex Ferguson
Image caption Alex Ferguson

Tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce kungiyar za ta iya lashe gasar Premier duk da tazarar maki takwas da ke tsakaninta da Arsenal mai jagorantar rukunin.

Nasarori biyu cikin wasanni uku na baya bayan nan da United ta samu na nuna cewa kungiyar da ke karkashin David Moyes ta farfado daga mafi munin koma bayan da ta samu cikin shekaru 14.

Alex Ferguson ya ce; "Mu kadai ne kungiyar da za ta iya tasowa daga kasa ta daga kofi saboda irin tarihin da mu ke da shi."

Ferguson, wanda yanzu haka darakta ne a kungiyar, ya sauka ne daga mukamin manaja a karshen kakar wasanni ta bara bayanda ya samowa kungiyar kofuna 38 a tsawon shekaru 27.

Magajinsa dai David Moyes na kokarin neman karbuwa wurin magoya bayan kungiyar bayanda ya fara kakar bana da kafar hagu.