"Ko dar ba na yi a Premier" - Wenger

wenger
Image caption Arsene Wenger

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce kayen da ta sha a hannun Chelsea a gasar kofin Capital One ba zai kawo ma ta cikas a gasar Premier ba.

Gunners ce kan gaba a rukunin Premier sai dai za ta karbi bakuncin Liverpool da Manchester United ne a wasanninta na gaba.

Tun bayan kayen da ta sha a wurin Aston Villa a wasan farko na bana, Arsenal ta yi nasara a wasanni 11 daga cikin 12 da ta buga kafin Borussia Dortmund ta lallasata a gasar cin kofin zakarun Turai a makon jiya.

A ranar Asabar ne Arsenal ta make Crystal Palace amma dukan da ta sha hannun Chelsea shi ne karo na farko tun watan Fabrairu da kungiyar ta gaza cin wasanni biyu a jere a gida.

Sai dai kuma Tottenham ce kawai Arsenal ta kara da ita cikin wadanda suka yi zarra a bara. Yanzu kuma za su karbi Liverpool kafin ziyartar Dortmund da Old Trafford. Daga nan kuma sai Southampton wacce ta casa Liverpool kuma ta yi kunnen doki da Manchester United.