Klopp ya sabunta kwantiragi a Dortmund

Jurgen Klopp
Image caption Kocin yana sa ran zai sake tabuka rawar gani a bana

Kocin Borussia Dortmund Jurgen Klopp ya sabunta kwantiraginsa da kungiyar, inda zai ci gaba da jagorantar ta har zuwa shekara ta 2018.

Kungiyar ta tattauna da Klopp, domin sabunta kwantaraginsa a bara , kuma yanzu ya amince da rattaba hannu a yarjejeniyar shekaru biyu.

Kocin ya fara horad da Dortmund a shekara ta 2008, ya kuma dauki kofuna biyu har da kofin da yayi nasarar dauka na cikin gida.

Dortmund ta kare a matsayi ta biyu a gasar Bundesliga biye da Bayern Munich a kakar bara, ta kuma rasa kofin zakarun Turai a wasan karshe da suka kara da kungiyar.