Najeriya na musun rage shekarun 'yan wasa

Fifa U 17
Image caption Gasar kofin duniya 'yan kasa da shekaru 17

Kocin 'yan kwallon Nigeria 'yan kasa da shekaru 17 Manu Garba, ya karyata zargin da kocin Iran ya yi ce wa 'yan wasan Nigeria sun yi karyar shekaru, bayan da suka yi rashin nasara da ci 4-1 a kofin duniya da Hadaddiyar Daular Larabawa ke karbar bakunci.

Nigeria da ta lashe kofin karo uku, ta casa Iran a filin wasa na Khalifa Bin Zayed da ke Al Ain, da zura kwallaye uku tun kafin a tafi hutu daga baya ta lashe wasan da ci 4-1 a karawar da tayi da wakiliyar nahiyar Asiya a wasan kasashe 16 da suka rage a gasar.

Bayan tashi daga wasan kocin Iran Ali Doustimehr ya zargi hakikanin shekarun 'yan wasan da suke wakiltar Afrika ta yamma.

Manu garba ya shedawa BBC ce wa "Ina ganin ya yi magana ne a lokacin da yake jin radadin cinyesu da muka yi, tun da mun fi su taka kwallo da kwarewa.

Ya kara da ce wa "dukkan 'yan wasanmu sun yi gwajin shekaru ta MRI, mun kuma sake wani gwajin wata guda kafin mu isa Hadaddiyar Daular Larabawa.