Chelsea ta dauko Traore

Bertrand Traore
Image caption Bertrand Traore

Chelsea ta dauki matashin yaron da ake yayi Bertrand Traore.

Sai da kungiyar ta Premier ta fafata da wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai kafin ta samu nasarar dauko dan wasan tsakiyar mai shekaru 18 daga kungiyarsa ta Association Jeunes Espoirs De Bobo-Dioulasso.

Dan wasan, wanda ya fara bugawa kasar Burkina Faso kwallo ya na shekara 15, ya amince da kwangilar shekaru hudu da rabi a Chelsea.

Traore ya buga wasnnin uku a ziyarar da Chelsea ta kai nahiyar Asia a matsayin gwaji.