Fifa ta amince a buga wasa a Alkahira

Image caption Ghana ta nuna fargaba a kan tsaro a Alkahira

Fifa ta amince a buga wasa tsakanin Masar da Ghana a birnin Alkahira a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za ayi a shekara ta 2014.

Fifa ta ce matakin ya biyo bayan tabbacin da gwamnatin Masar ta bayar a kan cewar akwai tsaro a birnin duk da fargabar da Ghana ta nuna.

A cewar gwamnatin Ghana, tun da an amincewa Al Ahly ta buga gasar kofin zakarun Afrika a Alkahira, to kenan babu wata matsalar tsaro wajen taka leda a birnin.

Sau biyu Ghana tana aikewa Fifa wasika don a sauya birnin da za a buga wasa tsakaninsu da Masar a ranar 19 ga watan Nuwamba.

A bugun farko da suka buga a birnin Kumasi, Ghana ta lallasa Masar daci 6 da 1.

Karin bayani