Manchester City ta doke Newcastle 2-0

Edin Dzeko
Image caption Edin Dzeko

Kwallayen da Alvaro Negredo da Edin Dzeko suka jefa a ragar Newcastle bayan karin lokaci ne suka sama wa Manchester City gurbi a cikin kungiyoyi takwas da suka rage a gasar cin kofin Capital One.

Wasan dai bai yi armashi ba, amma Newcastle ne suka fi samun dama sai dai golan City Costel Pantilimon ya kade kwallayen da Shola Ameobi da Papiss Cisse suka auna masa.

Bayan an kammala wasa canjaras, Negrodo ya zura kwallon farko a minti na 99 sannan Dzeko ya kara ta biyu a minti na 105.

Wannan nasarar ta ba City damar fuskantar Leicester da ke wasa a rukunin Championship a matakin daf da na kusa da na karshe.

Sai dai kwata kwata nasarar ta gaza irirn lallasawar da City ta yi wa Newcastle 4-0 a wasansu na farko a kakar Premier ta bana.