Liverpool za ta Champions - Werner

Suarez
Image caption Suarez

Mai kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Tom Werner ya ce kungiyar na da damar shiga gasar Zakarun Turai a badi.

A 2009 ta buga wasanta na karshe a gasar amma yanzu ta na mataki na uku a rukunin Premier bayan wasanni tara.

A bana dai sau daya kungiyar ta sha kaye a wasa kuma maki biyu ne tsakaninta da Arsenal da ke saman tebur.

Sai dai Werner ya ce ba'a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare domin kuwa sauran kungiyoyin da ke bugu Premier ba kanwar lasa ba ne.

Ya kuma bayyana fatan dan wasan gaba Luis Suarez zai ci gaba da zama a kungiyar.