NFF ta soma biyan Keshi albashinsa

Image caption Stephen Keshi

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta biya kocin Super Eagles Stephen Keshi wani bangare cikin albashin watanni bakwai da yake bin ta.

Keshi wanda ke bin NFF fiye da dala 217,000, a makon da ya gabata yace matakin tamkar "rashin mutun tashi ne".

Lamarin ya janyo saida hukumar wasannin Najeriya-NSC ta bukaci NFF ta gaggauta biyan albashin Keshi din.

Bayanai sun nuna cewar, an biya Keshi albashi na kusan watanni biyu daga cikin na watanni bakwai da yake bin hukumar.

Kakakin NFF, Ademola Olajire ya shaidawa BBC cewar "sona kokarin biyanshi duk sauran albashin da yake binmu".

Najeriya za ta kara da Ethiopia a ranar 16 ga watan Nuwamba a bugu na biyu na neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da za ayi a Brazil.

Karin bayani