United na farautar Brooklyn Beckham

Image caption Brooklyn da mahaifinsa Beckham

Manchester United na lura da irin ci gaba a fagen kwallon kafa da dan David Beckham, Brooklyn, ke samu.

Yaron mai shekaru 14 ya ziyarci wurin horon 'yan wasan United amma dai ba a bashi wata dama ba.

Za a baiwa Brooklyn damar ya yi horo sosai tare da United kafin a dauki hukunci a kansa.

Brooklyn ya taba horo da yara a kungiyar LA Galaxy da Chelsea da kuma QPR.

Karin bayani