Na kusa gajiyar Ferguson

Ericksson
Image caption Erickson da ya horadda Ingila da Manchester City

Steven Goran Erikson ya ce ya rattaba hannu a shekara ta 2002 domin karbar aiki a hannun Sir Alex Ferguson a Manchester United.

Ferguson ya yi ritaya, bayan shekaru 26 yana jagorancin kungiyar amma ya bayar da sanarwar niyyar sa ta yin ritaya a shekara ta 2002 kafin daga baya ya sauya ra ayi.

"Na saka hannu a yarjejeniya - ni ne sabon manajan United" in ji tsohon kocin Ingila Eriksson a sabon littafin da ya wallafa.

Direktan Wasanni na kungiyar Phil Townsend ya ce" ba mu karanta littafin nasa ba, saboda haka ba mu da wani jawabi da za mu yi."

Erikson dan Sweden mai shekaru 65 ya horar da Ingila daga 2001 zuwa 2006 daga baya ya koma kocin makwabciyarta Manchester City.