Bana tsoron barin Fulham — Martin Jol

Martin Jol
Image caption Wasa ya gaji haka 'yan kallo su soka ko su ki ka

Kocin Fulham Martin Jol ya ce baya cikin damuwa akan ko za a kore shi daga aiki, duk da rashin nasarar da kungiyarsa ta yi a wasanni uku a jere cikin sati, kuma na shida a gasar Premier ta bana.

Lokacin da Manchester United ta caskara Fulham a gida ranar Asabar data gabata da ci 3-1, 'yan kallo sun yi tayin ihu da kuwar "Jol ka tafi"

Kocin dan kasar Holland ya ce bana wani fargaba, a baya 'yan kallon sun ce dani Matin yazo bamu da fargaba.

Ya kara da ce wa "Wani lokacin ina damuwa idan 'yan kallon suna matsamin, amma haka yafi sauki da ace 'yan wasa suke matsawa."

Fulham bata tabuka rawar gani a Premier bana, musamman a filin wasanta dake Craven Cottage, a inda ta lashe wasa daya daga cikin wasanni biyar, ta koma matsayi na 15 duk da rashin nasara da tayi a hannun United.