Ina cike da bakin ciki da damuwa —Mourinho

Image caption Mourinho ya ce ba shi da kwarin gwiwa game da makomar kungiyar.

Kocin Chelsea, Jose Mourinho, ya ce yana cike da bakin ciki da damuwa bayan kungiyar ta sha kashi a hannun Newcastle a St James' Park.

Yoan Gouffran da Loic Remy ne suka zura kwallayen da suka bai wa Newcastle nasara.

Mourinho ya ce, ''Ina cike da bakin ciki saboda har yanzu ban gane dalilin da ya sa suka ci mu ba. Na yi zato sai a wasanmu na gaba za a doke mu.Mun buga wasa cike da kwarin gwiwa, duk da haka ba mu samu sakamako mai kyau ba''.

Duk da yake Chelsea sun yi nasara a wasanni shida da suka buga, Mourinho ya ce yana fargaba game da makomar kungiyar a Gasar Premier.

Karin bayani