Djokovic da Nadal za su fid da raini

Djokovic da Nadal
Image caption Djokovic da Nadal

Rafael Nadal da Novan Djokovic za su fafata domin fitar da zakaran wasan tennis na bana, inda birnin London ke karbar bakuncin gasar a karo na biyar.

Dan wasa na biyu Djokovic na fatan doke dan wasa na daya Nadal bayanda ya samu nasara a gasar Paris Masters ranar Lahadi.

Manyan 'yan wasan tennis din na duniya za su fara arangama ne ranar Talata a filin O2 Arena.

Andy Murray, dan wasan Birtaniya na farko da ya lashe kofin Wimbledon na maza cikin shekaru 77 bai samu shiga gasar ba kasancewar ya na fama da ciwon baya.