Fifa ta duba wasan Masar — Ghana

Jerome Valcke
Image caption Ghana na son sanin matakan tsaro da aka dauka

Ministan wasanni na Ghana ya bukaci ganawa da sakatare janar na Fifa Jerome Valcke akan matakan tsaro a wasan shiga gasar cin kofin duniya da zasu kara da Masar a Alkahira.

Elvis Afriyie Ankrah ya ce ma'aikatar wasanni tare da hukumar kwallon kafar Ghana har yanzu su na da tararrabin tsaro a wasan da za su kara ranar 19 ga watan Nuwamba.

Fifa ta ce a buga wasan a birnin da ake samun rikici, duk da Ghana ta nemi a sauya filin wasan har sau biyu.

Kimanin magoya bayan Ghana 30,000 za su halarci wasan, karo na farko da za a kara babban wasa a Alkahira kuma wasan farko da Masar za ta karbi 'yan kallo magoya baya da aka amince su shiga filin wasa tun lokacin da aka samu yamutsi a Port Said a Shekara ta 2012 inda sama da mutane 70 suka rasu.