"Kwallon kasa za mu yi wa Sweden"

Nigeria Supporters
Image caption Magoya bayan 'yan kwallon Nigeria

Kocin Matasa 'yan kasa da shekaru 17 na Nigeria, Manu Garba, ya ce wasan kasa za su bugawa Sweden idan sun zo karawa a wasan dab dana karshe na cin kofin duniya da Hadaddiyar Daulal Larabawa ke karbar bakunci a gobe.

Manu ya ce, "yan kwallon Sweden sun fi 'yan wasanmu tsawo da jiki, saboda haka a kasa za mu dinga gara kwallo.

Da yake hira da BBC, ya kara da cewa za su yi iya kokari su ga sun fara zura kwallo a raga, sannan za su kaucewa bugun kwana. Manu ya kara da cewa ya san wasan zai yi zafi.

A karawar farko da suka buga a cikin rukuni sai da Sweden ta fara zura kwallaye biyu kafin Nigeria ta farke aka tashi wasa 3-3.

Gobe ne Sweden da Nigeria za su kara a wasan kusa da na karshe a filin wasa na Rashid, bayan Argentina da Mexico sun tashi wasa.