"Tottenham na sakaci da lafiyar Lloris"

Tottenham Hotspurs
Image caption Tottenham Hotspurs

An zargi Tottenham da yin sakaci da lafiyar mai tsaron gida Hugo Lloris bayan kyaleshi ya cigaba da wasa duk da fita hayyacinsa da ya yi a karonsu da Everton.

Lloris dan kasar Faransa ya bugu ne a ka bayan da ya yi karo da gwiwar Romelu Lukaku a wasan ranar Lahadi da aka tashi 0-0.

Kocin Spurs Andre Villas-Boas ya kare matakin da ya dauka na barin Lloris ya cigaba da wasa.

Sai dai kungiyar kula da masu raunin kwakwalwa Headway ta ce kungiyar ta nuna halin "ko-in-kula" ga lafiyar Lloris.

Kakakin kungiyar Luke Griggs ya ce: "Duk lokacin da dan wasa ya samu buguwa a ka har ta kai ya fita hayyacinsa, abu ne mai matukar muhimmanci a nema masa agajin gaggawa."