Ba rabon Ingila a Brazil 2014 - Eriksson

Sven Goran Eriksson
Image caption Sven Goran Eriksson

Tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson ya ce kasar ba za ta iya cin kofin kwallon kafa na duniya a Brazil ba.

Dan kasar Sweden din, da ya jagoranci Ingila zuwa matakin daf da na kusa da na karshe a 2002 da 2006 ya shaidawa BBC cewa: "Akwai matasan 'yan wasa da dama da ke shigowa. Ba mamaki su yi nasara a Rasha."

Kungiyar karkashin Roy Hodgson ta samu damar zuwa Brazil ne bayanda ta yi nasara a rukuninta, amma dai ta samu kanta cikin kasashe masu martaba ta biyu a tsarin fitar da jadawalin kasashen da za su kara da juna da za'a gudanar 6 ga Disamba.

Za su kafa tarihi idan har suka maimaita nasararsu tilo da suka taba yi a 1966 kasancewar babu wata kasar Turai da ta taba daga kofin a Amurka ta Kudu.

Shi ma shugaban hukumar kwallon kafa ta Ingila Greg Dyke ya fid da ran kasar za ta yi nasara a gasar ta badi, inda ya ke fatan lashe gasar 2022.