Man City ta gargadi CSKA game da Toure

Pellegrini da Toure
Image caption Pellegrini da Toure

Kocin Manchester City Manuel Pellegrini ya gargadi magoya bayan CSKA Moscow su guji maimaita zagin wariyar launin fatar da suka yi wa dan wasan tsakiya Yaya Toure ranar Talata.

Kungiyoyin biyu za su sake karawa ne a gasar cin kofin zakarun Turai makonni biyu bayanda aka muzgunawa Toure a wasan da City ta sami nasara 2-1, abinda ya jawo hukumar Uefa ta hukunta kungiyar ta Rasha.

Hukuncin dai ya tanadi rufe wani sashe na filin wasan CSKA a lokacin da kungiyar za ta karbi bakuncin Bayern Munich ranar 27 ga Nuwamba.

A cewar Pellegrini wajibi ne magoya bayan kungiyar su nuna halayya ta gari saboda "su zasu karbi bakuncin gasar kofin duniya a kasarsu" a 2018.

CSKA Moscow dai ta dage cewa an zuzuta batun wariyar launin fatar da aka yi wa Toure kuma hukuncin da Uefa ta dauka ya yi tsanani da yawa.