Safa ta haramtawa jami'ai 15 kwallo har abada

Danny Jordaan
Image caption Danny Jordaan

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu (safa) ta haramtawa jami'anta 15 aiki har abada saboda kokarin kai karar hukumar da suka yi, abinda ya sabawa dokar Fifa.

Matakin na Safa ya danganci korafe-korafen jami'anta daga lardin Free State game da zaben Danny Jordaan a matsayin shugaban hukumar a Satumba.

Hukumar ta ce kamata ya yi jami'an su kai kukansu gare ta.

Safa ta bayyana jami'an a matsayin "bata-gari" sannan ta haramta su duk wani aiki da ya shafi kwallon kafa tsawon rawuyarsu.

A ranar 28 ga Satumba ne aka zabi Jordaan, wanda ya jagoranci shirya gasar kwallon kafa ta duniya da 2010 a matsayin shugaban Safa.