An samu Sascha Riether da laifi

Sascha Riether
Image caption Dan wasan farko da aka samu da laifi

Dan wasan Fulham Sascha Riether ya zamo dan wasa na farko da aka samu da laifi a sabon tsarin kallon wasa bayan an gama.

Dan kwallon mai tsaron baya mai shekaru 30, ya kaiwa dan wasan Manchester United Adnan Januzaj keta a karawar da Fulham ta yi rashin nasara da ci 3-1, amma alkalin wasa bai ga ketar ba.

A sabon tsarin, fitattun alkalai uku sun kalli wasan kuma suka tuhumci Riether da karya dokar wasa.

An baiwa Riether damar daukaka kara a yau, bisa zarginsa da ake masa.

An kirkiro sabon tsarin ne bayan da dan kwallon Wigan Callum McManaman ya kaucewa hukunci akan ketar da ya yiwa dan kwallon Newcastle Massadio a kakar wasan bara.