Tarihin Dan kwallon Ivory Coast Yaya Toure

Image caption Yaya Toure

Mutumin da kowa ya shaida a matsayin daya daga cikin ‘yan wasan tsakiyar da suka fi kwarewa a cikin sa’anninsa, Yaya Toure, gwarzon dan wasa ne – Janar ne shi a filin kwallo wanda kowa ke girmamawa.

Ya shiga kungiyarsa ta Manchester City ne a 2010 kuma tuni ya lashe Gasar Premier – a karo na farko da kungiyar ta ci Kofin cikin shekaru 44 – tare da Kofin FA da Community Shields.

Toure ya ci kwallaye 23 a wasanni 109 da ya bugawa City, ciki kuwa har da wasu luguden bugun tazara masu matukar kayatarwa, kuma kawo yanzu shi ne dan wasa mafi muhimmanci a kungiyar.

Ya koma City ne daga Barcelona, inda ya kwashe shekaru uku kuma ya tara dimbin nasarori da suka hada da Kofin Laliga biyu, Kofin Zakarun Turai, Uefa Super Cup, da kuma Kofin Fifa World Club Cup.

Dan wasan mai shekaru 30 ya daga Kofin kasar Girka a kungiyar Olympiakos da kuma Kofin kwallon kafa na kasar Ivory Coast a kungiyar ASEC Mimosas.

Babban takaicin Toure ya zo ne a wasannin da ya bugawa kasarsa inda kwararrun ‘yan wasan da kasar ke alfahari da su suka kasa ciwo Kofin da aka sa mu su rai. Nasarar da Zambia ta yi akansu a wasan karshe na Gasar cin Kofin Afirica ta 2012 na daga cikin manyan abubuwan ban mamaki a tarihin kwallon kafa na Africa.

Bayan cikarsa shekaru 30, Toure bai fara nuna alamun gazawa ba kuma ya fara kakar wasan bana a City da kafar dama, inda tuni ya zura kwallaye bakwai tare da nuna kwarewa da bajinta a dukkan wasanninsa.

Mutumin da ya lashe gasar gwarzon dan kwallon Afirka sau biyu, Toure ne kadai dan wasan Afrika a cikin jerin ‘yan wasa 23 da hukumar Fifa ta fitar da sunayensu domin takarar cin gasar gwarzon dan kwallon kafa na duniya.