"Ban ga dalilin surutu akan Lloris ba"

Andre Villa Boas
Image caption Villa Boas ya ce wasu ne ke neman suna da batun

Kocin Tottenham Andre Villa Boas ya bayyana mamakinsa ga me da yamadidin da ake yi don ya bar gola Hugo Lloris ya koma wasa bayan da ya fita daga hayyacinsa.

Dan kwallon Faransa mai shekaru 26, ya yi karo da Romelu Lukaku, lokacin da suka kara da Everton aka tashi wasa babu ci a ranar Lahadi data gabata.

An soki Tottenham da suka amince golan ya koma wasa.

"Ina nan a kan hukuncin dana yanke da kuma matakin da likitocin kungiya suka dauka, domin sunyi komai bisa ka'ida" inji Villas-Boas.

"Wa su mutane ne kawai ke amfani da labarin don neman suna. Ba su da masaniyar me yake faruwa a fili musamman irin wannan yanayin."