Arsenal za ta iya lashe kofin Turai

Arsenal
Image caption Kloop ya yaba da kwallon Arsenal

Kocin Borussia Dortmund Jurgen Klopp ya ce Arsenal zata iya lashe kofin zakarun Turai matukar ba za ta hadu da Bayern Munich ba, lokacin da aka fidda jadawalin wasan sili biyu kwale.

Aaron Ramsey shi ne ya zura kwallo lokacin da Arsenal ta doke Dortmund da ci 1-0 ranar Laraba, Arsenal ta ci gaba da jagorantar rukunin na F duk da saura wasanni biyu a kammala wasannin cikin rukuni.

Dortmund ta sa ran zata lashe wasa na takwas a gida a gasar cin kofin zakarun Turai, kuma bata taba rashin nasara a hannun kungiya daga Ingila ba.

Kloop ya ce "zasu iya lashe kofin matukar basu hadu da Bayern Munich ba, suna da matasan 'yan wasa da suka kware da taka kwallo."

Kwallon da Ramsey ya zura itace ta 11 da ya zura a wasanni 17 da ya bugawa Arsenal.