Martinez: kar a bamu wuka da nama

Roberto Martinez
Image caption Bai kamata a bar mana wuka da nama ba

Kocin Everton Roberto Martinez ya goyi da bayan a hana kociyoyi yanke hukunci ko dan wasa zai iya ci gaba da wasa idan ya fita daga hayyacin sa.

Golan Tottenham Hugo Lloris ya fita daga hayyacinsa bayan da ya yi karo da dan kwallon Everton mai zura kwallo Romelu Lukaku, amma ya ci gaba da wasa bayan da aka dauki lokaci mai tsawo Likitoci su ka duba lafiyarsa.

Kocin Tottenham Villas-Boas ya sha suka da ya amince Lloris ya koma kwallo.

Martinez ya ce "idan likitoci suka bada tabbacin a canja dan kwallon da ya fita daga hayyacinsa, ya kamata mu duba mu kuma yi amfani da shawarar da suka bada. Ina ganin ba koci ne ya dace ya yanke hukuncin dan wasa ya ci gaba da wasa ba ko a cire shi daga wasa bayan ya fita hayyacinsa.