Tarihin dan kwallon Burkina Faso Jonathan Pitroipa

Image caption Jonathan Pitroipa

Babu wanda ya taba sa ran Jonathan Pitroipa zai shiga jerin ‘yan wasan da ke takarar gwarzon dan kwallon kafa na BBC kafin a take wasa a gasar cin kofin Africa ta bana, inda aka sa Burkina Faso cikin wani rukuni mai wuya tare da Zambia da Nigeria.

Sai dai ba wai kawai Chipolopolo masu kare kambun Stallions din suka doke ba, sai da suka zama jagorar rukuninsu sama da Nigeria.

A wasan karshe dai Super Eagles ne suka yi nasara kan Burkina Faso da kyar amma duk da haka Pitroipa – ba wani dan Nigeria ba – shi ne ya zama gwarzon gasar.

Tun da fari dan wasan gefen na Rennes ya fara rawar gani inda ya bada kwallon da aka farke 1-1 a wasan farko da suka buga da Nigeria, kuma a karon gaba ya kara kwazo inda ya ci daya kuma ya bada kwallaye biyu aka ci a wasan da su 10 suka ragargaji Ethiopia 4-0.

Wannan ne karo na farko da Stallions suka taba cin wasa a gasar nahiyar Afrika tun bayan da suka kai matakin daf da na karshe a 1998. Daga nan kuma Pitroipa sai da ya kasu har matakin kusa da na karshe bayanda ya ci 1-0 a Karin lokacin da aka yiwa wasansu da Togo.

Bayan da aka ba shi jan kati bisa kuskure a wasan kusa da na karshe da suka doke Ghana, tsohon dan wasan na Hamburg ya buga wasan karshe bayan kankare masa kati, sai dai bai yi wani tasiri ba a wasan da aka cinye su 1-0.

Duk da haka, ya ci gaba da nuna kuzari a wasannin neman shiga gasar kwallon kafa ta duniya, inda Stallions ta zama zakara a rukuninta bayan ta sha fama da kalubale, sannan ya jefa kwallo mai matukar muhimmanci a nasarar 3-2 da suka samu kan Algeria.

A matakin kulob kuwa, Pitroipa yak are kakar wasa ta 2012/13 da kwallaye bakwai inda Rennes ta zo ta 13 kuma ta isa wasan karshe a karo na farko a gasar League Cup ta Faransa, inda ta sha kaye a hannun St Etienne.